📖 Zabura 103
-
1
Yabi Ubangiji, ya raina; dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.
-
2
Yabi Ubangiji, ya raina, kada kuma ka manta dukan alheransa,
-
3
wanda yake gafarta dukan zunubai yake kuma warkar da dukan cututtuka,
-
4
wanda ya fanshi ranka daga rami ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,
-
5
Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.
-
6
Ubangiji yana aikata adalci da kuma gaskiya ga duk waɗanda aka danne.
-
7
Ya sanar da hanyoyinsa wa Musa, ayyukansa ga mutanen Isra’ila.
-
8
Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.
-
9
Ba zai yi ta zargi ba ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;
-
10
ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.
-
11
Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;
-
12
kamar yadda gabas yake daga yamma, haka ya cire laifofinmu daga gare mu.
-
13
Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa, haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;
-
14
gama ya san yadda aka yi mu, ya tuna cewa mu ƙura ne.
-
15
Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa da suke haɓaka kamar fure a gona;
-
16
iska kan hura a kansa sai ya ɓace ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake.
-
17
Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,
-
18
tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.
-
19
Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama, masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka.
-
20
Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa, ku jarumawa masu yi masa aiki, waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.
-
21
Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama, ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.
-
22
Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa ko’ina a mulkinsa. Yabi Ubangiji, ya raina.