📖 Zabura 100
-
1
Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.
-
2
Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.
-
3
Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.
-
4
Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa.
-
5
Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.