1¶ Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba.
2Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Ya yi mulki daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa, Kogin Yabbok, wanda yake iyakar Ammonawa. Wannan ya haɗa da rabin Gileyad.
3Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga.
4Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.
5Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.
6Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.
7¶ Waɗannan su ne sarakuna da kuma ƙasashen da Yoshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammancin Urdun, daga Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa Seyir. Yoshuwa ya raba ƙasarsu ta zama gādo ga Isra’ilawa bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila.
8Ƙasar ta haɗa da ƙasar kan tudu, filayen arewanci, Araba, gangaren Dutse, da jejin, da kuma Negeb, wato, ƙasashen Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa.
9Sarkin Yeriko, ɗaya sarkin Ai (kusa da Betel), ɗaya
10sarkin Urushalima, ɗaya sarkin Hebron, ɗaya
11sarkin Yarmut, ɗaya sarkin Lakish, ɗaya
12sarkin Eglon, ɗaya sarkin Gezer, ɗaya
13sarkin Debir, ɗaya sarkin Bet-Gader, ɗaya
14sarkin Horma, ɗaya sarkin Arad, ɗaya
15sarkin Libna, ɗaya sarkin Adullam, ɗaya
16sarkin Makkeda, ɗaya sarkin Betel, ɗaya
17sarkin Taffuwa, ɗaya sarkin Hefer, ɗaya
18sarkin Afek, ɗaya sarkin Sharon, ɗaya
19sarkin Madon, ɗaya sarkin Hazor, ɗaya
20sarkin Shimron Meron, ɗaya sarkin Akshaf, ɗaya
21sarkin Ta’anak, ɗaya sarkin Megiddo, ɗaya
22sarkin Kedesh, ɗaya sarkin Yokneyam a Karmel, ɗaya
23sarkin Dor (A Nafot Dor), ɗaya sarkin Goyim a Gilgal, ɗaya
24sarki Tirza, ɗaya. Duka-duka dai sarakuna talatin da ɗaya ne.