1Ina ƙaunataccenki ya tafi, yake mafiya kyau cikin mata? Wace hanya ce ƙaunataccenki ya bi, don mu taimake ki nemansa.
2Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa, zuwa inda fangulan kayan yaji suke, don yă yi kiwo a cikin lambun don kuma yă tattara furen bi-rana.
3Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne; yana kiwo a cikin furen bi-rana.
4Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, kyakkyawa kuma kamar Urushalima, mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.
5Ki kau da idanu daga gare ni; gama suna rinjayata. Gashinki yana kama da garken awakin da suke gangarawa daga Gileyad.
6Haƙoranki suna kama da garken tumakin da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai.
7Kumatunki sun yi kamar rumman da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.
8Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can, da ƙwarƙwarai tamanin da kuma budurwai da suka wuce ƙirge;
9amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take, tilo kuwa ga mahaifiyarta, ’yar lele ga wadda ta haife ta. ’Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka; sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta.
10Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir? Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, mai daraja kamar taurari a jere?
11Na gangara zuwa cikin itatuwan almon don in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari, don in ga ko inabi sun yi ’ya’ya ko rumman suna fid da furanni.
12Kafin in san wani abu, sha’awarta ta sa ni a cikin keken yaƙin sarkin mutanena.
13Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya; ki dawo, ki dawo, don mu dube ki!