1Ni furen bi-rana ne na Sharon, furen bi-rana na kwari.
2Kamar furen bi-rana a cikin ƙayayyuwa haka ƙaunatacciyata take a cikin ’yan mata.
3Kamar itacen gawasa a cikin itatuwan jeji haka ƙaunataccena yake a cikin samari. Ina farin ciki in zauna a inuwarsa, ’ya’yan itacensa suna da daɗin ɗanɗanon da nake so
4Ya kai ni babban zauren da ake liyafa, ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.
5Ka ƙarfafa ni da zabibi ka wartsake ni da gawasa, gama ina suma don ƙauna.
6Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni.
7’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.
8Saurara! Ƙaunataccena! Duba! Ga shi ya iso, yana tsalle a duwatsu, yana rawa a bisa tuddai.
9Ƙaunataccena yana kama da barewa ko sagarin ƙishimi Duba! Ga shi can tsaye a bayan katangarmu, yana leƙe ta tagogi, yana kallo ta cikin asabari.
10Ƙaunataccena ya yi magana ya ce mini, “Tashi, ƙaunatacciyata, kyakkyawata, ki zo tare da ni.
11Duba! Damina ta wuce; ruwan sama ya ɗauke ya kuma ƙare.
12Furanni sun hudo a duniya; lokaci yin waƙa ya zo, ana jin kukan kurciyoyi ko’ina a ƙasarmu.
13Itacen ɓaure ya fid da ’ya’yansa da sauri; tohon inabi suna ba da ƙanshinsu. Tashi, zo, ƙaunatacciyata; kyakkyawata, zo tare da ni.”
14Kurciyata a kogon dutse, a wuraren ɓuya a gefen dutse, nuna mini fuskarki, bari in ji muryarki; gama muryarki da daɗi take, fuskarki kuma kyakkyawa ce.
15Kama mana ɓeraye, ƙananan ɓerayen da suke lalatar da gonakin inabi, gonakin inabinmu da suke cikin yin fure.
16Ƙaunataccena nawa ne ni kuma tasa ce; yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana.
17Sai gari ya waye inuwa kuma ta watse, ka juye, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kamar sagarin ƙishimi a kan tuddai masu ciyawa.