1¶ Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki.
2Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata.
3Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ’yan’uwana, waɗannan na kabilata,
4mutanen Isra’ila. Su ne Allah ya mai da su ’ya’yansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawura.
5Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin.
6¶ Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ila na gaske ba.
7Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama ’ya’yan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”
8Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ’ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.
9Ga yadda aka yi alkawarin nan, “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za tă haifi ɗa.”
10¶ Ba ma haka kaɗai ba, ’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku.
11Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa,
12ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.”
13Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”
14¶ Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan!
15Gama ya ce wa Musa, “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai, zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”
16Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah.
17Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.”
18Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.
19¶ Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?”
20Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ”
21Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?
22¶ Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka?
23Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka
24har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai?
25Kamar yadda ya faɗa a Hosiya. “Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba; zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,”
26kuma, “Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba,’ za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’ ”
27Ishaya ya ɗaga murya game da Isra’ila ya ce, “Ko da yake yawan Isra’ilawa yana kama da yashi a bakin teku, ragowa ce kaɗai za su sami ceto.
28Gama Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.”
29Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa. “Da ba don Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana zuriya ba, da mun zama kamar Sodom, da mun kuma zama kamar Gomorra.”
30¶ Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya;
31amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba.
32Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.”
33Kamar yadda yake a rubuce, “Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe da kuma dutsen da yake sa su fāɗi wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”