1¶ To, fa, shugabannin mutane suka zauna a Urushalima, sauran mutanen kuma suka jefa ƙuri’a don su kawo mutum ɗaya daga kowane mutum goma don su zauna a Urushalima, birni mai tsarki, yayinda sauran tara suka zauna a garuruwansu.
2Sai mutane suka yaba wa dukan mutanen da suka ba da kansu da yardar rai su zauna a Urushalima.
3Waɗannan su ne shugabannin yankuna waɗanda suka zauna a Urushalima (ko da yake waɗansu Isra’ilawa, da firistoci, da Lawiyawa, da ma’aikatan haikali, da zuriyar bayin Solomon, suka yi zama a cikin garuruwan Yahuda, kowanne a mallakarsa cikin garuruwa dabam-dabam,
4yayinda sauran mutane daga Yahuda da Benyamin suka zauna a Urushalima). Daga zuriyar Yahuda akwai, Atahiya ɗan Uzziya, ɗan Zakariya, ɗan Amariya, ɗan Shefatiya, ɗan Mahalalel, wani zuriyar Ferez;
16da Shabbetai, da kuma Yozabad, biyu cikin shugabanni Lawiyawa waɗanda suke da nawayar aiki waje da gidan Allah.
17Sai kuma Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zabdi, ɗan Asaf, shugaban da yake bi da hidimar godiya da kuma addu’a. Sai Bakbukiya, na biyu a cikin ’yan’uwansa; da Abda ɗan Shammuwa, ɗan Galal, ɗan Yedutun.
18Lawiyawan da suke cikin birni mai tsarki sun kai 284.
19Matsaran ƙofofi kuwa su ne, Akkub, da Talmon, da ’yan’uwansu waɗanda suke tsaron ƙofofi, su 172 ne.
20¶ Sauran Isra’ilawa tare da firistoci, da Lawiyawa sun kasance a dukan garuruwan Yahuda, kowanne a mallakar kakansa.
21¶ Ma’aikatan haikali sun zauna a kan tudun Ofel. Ziha, da Gishfa ne suke lura da su.
22¶ Babban shugaban Lawiyawa a Urushalima shi ne Uzzi ɗan Bani, ɗan Hashabiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mika. Uzzi yana ɗaya daga zuriyar Asaf, waɗanda suke mawaƙan da suke da nawayar hidima a gidan Allah.
23Mawaƙa sun bi umarnan sarki, a kan abin da za su yi kowace rana.
24¶ Fetahahiya ɗan Meshezabel, ɗaya daga zuriyar Zera ɗan Yahuda ne, wakilin sarki cikin dukan al’amuran da suka shafi mutane.
25¶ Game da ƙauyukan da filayensu, waɗansu mutanen Yahuda suka zauna a Kiriyat Arba da ƙauyukanta, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta.
26Akwai su kuma a Yeshuwa, da Molada, da Bet-Felet,
27da Hazar Shuwal, da Beyersheba da ƙauyukanta.
28Akwai su a Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta.
29Suna nan kuma a En Rimmon, da Zora, da Yarmut,
30da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da kuma Azeka da ƙauyukanta. Saboda haka sun yi zama tun daga Beyersheba har zuwa Kwarin Hinnom.
31¶ Zuriyar mutanen Benyamin daga Geba sun zauna a Mikmash, da Aiya, da Betel da ƙauyukanta,
32da Anatot, da Nob, da Ananiya,
33da Hazor, da Rama, da Gittayim,
34da Hadid, da Zeboyim, da Neballat,
35da Lod, da Ono, da kuma a Kwarin Masu sana’a.
36¶ Waɗansu gundumomin Lawiyawan Yahuda sun zauna a Benyamin.