1Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe. Ki tsare mafaka, ki yi gadin hanya ki sha ɗamara ki tattaro dukan ƙarfinki!
2Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub, kamar ta Isra’ila, ko da yake masu washewa sun washe su suka kuma lalatar da inabinsu.
3Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya a ranar da aka shirya su; ana kaɗa māsu da bantsoro.
4Kekunan yaƙi sun zabura a tituna, suna kai da kawowa a dandali. Suna walƙiya kamar tocila suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.
5Ninebe ta tattara rundunarta, duk da haka sun yi ta tuntuɓe a kan hanyarsu. Sun ruga zuwa katangan birnin, sun sanya garkuwar kāriya a inda ya kamata.
6An buɗe ƙofofin rafuffukan sai wurin ya rurrushe.
7An umarta cewa birnin za tă tafi bauta, za a kuma yi gaba da su. Bayi ’yan mata suna kuka kamar tattabaru suna buga ƙirjinsu.
8Ninebe tana kama da tafki, wanda ruwanta yana yoyo. Suna kuka suna cewa, “Ku tsaya! Ku tsaya,” amma ba wanda ya waiga.
9A washe azurfa; a washe zinariya; dukiyarsu ba ta da iyaka, arzikinsu kuma ba ya ƙarewa.
10Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa, jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare!
11Ina kogon zakokin nan yake yanzu, inda suka ciyar da ’ya’yansu, inda zaki da zakanya sukan shiga, da ’ya’yansu, ba mai damunsu
12Zaki ya kashe abin da ya ishe ’ya’yansa ya kuma murɗe wuyan dabbobi ya cika wurin zamansa da abin da ya kama ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe.
13“Ina gāba da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ƙone kekunan yaƙinki, takobi kuma zai fafare ’ya’yan zakokinki. Ba kuma zan bar miki namun jejin da za ki kashe a duniya ba. Ba kuwa za a ƙara jin muryar ’yan saƙonki ba.”