1¶ Wani lokaci, da ya sāke shiga majami’a, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu.
2Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci.
3Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, ‹“Tashi ka tsaya a gaban kowa.”›
4¶ Sai Yesu ya tambaye su ya ce, ‹“Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?”› Amma suka yi shiru.
5¶ Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, ‹“Miƙo hannunka.”› Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
6Sai Farisiyawa suka fita, suka fara ƙulla shawara da mutanen Hiridus yadda za su kashe Yesu.
7¶ Yesu da almajiransa suka janye zuwa tafkin, taro mai yawa kuwa daga Galili ya bi shi.
8Mutane da yawa daga Yahudiya, da Urushalima, da Edom, da kuma yankunan da suke ƙetaren Urdun, da kewayen Taya, da Sidon suka zo wurinsa, don sun ji dukan abubuwan da yake yi.
9Saboda taron, sai ya ce wa almajiransa su shirya masa ƙaramin jirgin ruwa, don kada mutane su matse shi.
10Gama ya warkar da mutane da yawa, masu cututtuka suka yi ta ƙoƙarin zuwa gaba, don su taɓa shi.
11Duk sa’ad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.”
12Amma yakan tsawata musu, kada su shaida ko wane ne shi.
13¶ Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa.
14Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi,
15don kuma su sami ikon fitar da aljanu.
16Ga sha biyun da ya naɗa. Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus);
17Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”);