📖 Makoki 5
-
1
Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu; duba, ka ga kunyar da muka sha.
-
2
An ba wa baƙi gādonmu, gidajenmu kuma aka ba bare.
-
3
Mun zama marayu marasa ubanni, uwayenmu kamar gwauraye.
-
4
Dole mu sayi ruwan da muke sha; sai mun biya mu sami itace.
-
5
Masu fafararmu sun kusa kama mu; mun gaji kuma ba dama mu huta.
-
6
Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya don mu sami isashen abinci.
-
7
Kakanninmu sun yi zunubi kuma ba sa nan yanzu, mu ne aka bari muna shan hukuncinsu.
-
8
Bayi suna mulki a kanmu, kuma ba wanda zai ’yantar da mu daga hannuwansu.
-
9
Muna samun burodi a bakin rayukanmu domin takobin da yake a jeji.
-
10
Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu, muna jin zazzaɓi domin yunwa.
-
11
An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona, da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda.
-
12
An rataye ’ya’yan sarakuna da hannuwansu; ba a ba wa dattawa girma.
-
13
Samari suna faman yin niƙa; yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace.
-
14
Dattawan sun bar ƙofar birnin, samari sun daina rera waƙa.
-
15
Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki.
-
16
Rawani ya fāɗi daga kanmu. Kaiton mu gama mun yi zunubi!
-
17
Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi; domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe
-
18
gama Tudun Sihiyona ya zama kufai, sai diloli ke yawo a wurin.
-
19
Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada; kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani.
-
20
Don mene ne kake mantawa da mu koyaushe? Me ya sa ka yashe mu da jimawa?
-
21
Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo; ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā
-
22
sai dai in ka ƙi mu gaba ɗaya kana fushi da mu fiye da yadda za a iya aunawa.