📖 Makoki 3
-
1
Ni ne mutumin da ya ga azaba ta wurin bulalar fushin Ubangiji.
-
2
Ya kore ni, ya sa na yi tafiya a cikin duhu maimakon a cikin haske;
-
3
ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni sau da sau, dukan yini.
-
4
Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa ya kuma karya ƙasusuwana.
-
5
Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni da baƙin ciki da kuma wahala.
-
6
Ya sa na zauna a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu da jimawa.
-
7
Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba; Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.
-
8
Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata.
-
9
Ya tare hanyata da tubula na duwatsu; ya sa hanyata ta karkace.
-
10
Kamar beyar da take a laɓe tana jira, kamar zaki a ɓoye,
-
11
ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni ya bar ni ba taimako.
-
12
Ya ja kwarinsa ya sa in zama abin baratarsa.
-
13
Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa.
-
14
Na zama abin dariya ga mutanena duka; suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.
-
15
Ya cika ni da kayan ɗaci ya gundure ni da abinci mai ɗaci.
-
16
Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa; ya tattake ni cikin ƙura.
-
17
An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata.
-
18
Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”
-
19
Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai.
-
20
Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina.
-
21
Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba.
-
22
Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
-
23
Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne.
-
24
Na ce wa kaina, “ Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.”
-
25
Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi;
-
26
yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.
-
27
Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro.
-
28
Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi.
-
29
Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege.
-
30
Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci.
-
31
Gama Ubangiji ba ya yashe mutane har abada.
-
32
Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa.
-
33
Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.
-
34
Bai yarda a tattake ’yan kurkuku a ƙasa ba,
-
35
ko kuma a danne wa mutum hakkinsa a gaban Maɗaukaki,
-
36
ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?
-
37
Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba?
-
38
Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?
-
39
Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?
-
40
Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji.
-
41
Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu ga Allah na cikin sama, mu ce,
-
42
“Mun yi zunubi mun yi tawaye ba ka kuwa gafarta ba.
-
43
“Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu; ka karkashe mu ba tausayi.
-
44
Ka rufe kanka da gajimare don kada addu’armu ta kai wurinka.
-
45
Ka mai da mu tarkace da juji a cikin mutane.
-
46
“Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana marar daɗi.
-
47
Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.”
-
48
Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena.
-
49
Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa.
-
50
Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani.
-
51
Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina.
-
52
Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu.
-
53
Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami suka kuma jajjefe ni da duwatsu;
-
54
ruwaye suka rufe kaina, sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.
-
55
Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi.
-
56
Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”
-
57
Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”
-
58
Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina.
-
59
Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!
-
60
Ka ga zurfin ramakonsu, da duk mugun shirin da suke yi mini.
-
61
Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini
-
62
Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai game da ni duk yini.
-
63
Dube su! A zaune ko a tsaye, suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu.
-
64
Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji, domin abin da hannuwansu suka yi.
-
65
Ka sa yana ta rufe zuciyarsu, kuma bari la’anarka ta bi su.
-
66
Ka fafare su cikin fushi ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.