14wawa kuma yakan yi ta surutu. Ba wanda ya san abin da zai zo wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?
15Aikin wawa yakan gajiyar da shi, har bai san hanyar zuwa gari ba.
16Kaitonki, ya ke ƙasa wadda sarkinki bawa ne wadda kuma hakimanta ke ta shagali tun da safe.
17Mai albarka ce, ya ke ƙasa wadda sarkinki haifaffen gidan sarauta ne, wadda hakimanta suke samun abincinsu a daidai lokacin don samun ƙarfi ba don buguwa ba.
18In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa, in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo.
19Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma kuɗi ne amsar kome.
20Kada ka zagi sarki ko da a cikin tunaninka ne, ko ka zagi mai arziki ko da a ɗakin kwananka ne, gama tsuntsun sararin sama zai iya ɗauki maganarka, tsuntsu mai fikafikai zai sanar da abin da ka ce.