1¶ Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya.
2Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin.
3Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba.
4Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya.
5A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu?
6Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa,
7‹‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’› ”
8Sai suka tuna da maganarsa.
9¶ Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa.
10Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su.
11Amma ba su gaskata matan ba, domin sun ɗauki kalmominsu wani zancen banza ne.
12Duk da haka, Bitrus ya tashi a guje zuwa kabarin. Da ya sunkuya, sai ya ga ƙyallayen lilin kaɗai a kwance. Sai ya koma yana tunani a ransa, a kan abin da ya faru.
13¶ A wannan rana kuma, biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani ƙauye, da ake kira Emmawus, da suke kusan mil bakwai daga Urushalima.
14Suna magana da juna a kan dukan abubuwan da suka faru.
15Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su.
16Amma ba a ba su ikon gane shi ba.
17¶ Sai ya tambaye, su ya ce, ‹“Mene ne kuke tattaunawa da juna a cikin tafiyarku?”› Suka tsaya shiru, da damuwa a fuskarsu.
18¶ Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a cikin kwanakin nan ba?”
19¶ Sai ya yi tambaya, ‹“Waɗanne abubuwa?”› Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane.
20¶ Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi.
21Amma da, muna sa zuciya cewa, shi ne wanda zai fanshi Isra’ila. Bugu da ƙari kuma yau kwana uku ke nan tun da wannan abin ya faru.
22Har wa yau, waɗansu daga cikin matanmu sun ba mu mamaki. Sun je kabarin da sassafen nan,
23amma ba su sami jikinsa ba. Sun dawo sun faɗa mana cewa, sun ga wahayi na mala’iku, da suka ce yana da rai.
24Sa’an nan, waɗansu abokanmu suka je kabarin, suka kuma tarar da kome kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.”
25¶ Sai ya ce musu, ‹“Ashe, ku marasa azanci ne, masu nauyin zuciyar gaskata, da dukan abin da annabawa suka faɗa!›
38Sai ya ce musu, ‹“Don me kuke damuwa, kuke kuma shakka a zuciyarku?›
39‹Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”›
40¶ Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.
41Kuma har yanzu, suna cikin rashin gaskatawa, saboda murna da mamaki, sai ya tambaye su, ‹“Kuna da abinci a nan?”›
42Suka ba shi ɗan gasasshen kifi,
43ya karɓa ya ci a gabansu.
44¶ Ya ce musu, ‹“Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”›
45¶ Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi.
46Ya ce musu, ‹“Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu.›
47‹Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.›
48‹Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.›
49‹Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”›
50¶ Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.
51Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama.
52Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai.
53Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.