📖 Karin Magana 9
-
1
Hikima ta gina gidanta; ta yi ginshiƙansa bakwai.
-
2
Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta; ta kuma shirya teburinta.
-
3
Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira daga wurare masu tsayi na birnin.
-
4
“Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!” Tana faɗa wa marasa hankali.
-
5
“Ku zo, ku ci abincina da ruwan inabin da na gauraye.
-
6
Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu; yi tafiya a hanyar fahimi.
-
7
“Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci.
-
8
Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka; ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.
-
9
Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima; ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa.
-
10
“Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima, sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
-
11
Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa, za a kuwa ƙara wa ranka shekaru.
-
12
In kana da hikima, hikimarka za tă ba ka lada; in kai mai ba’a ne, kai kaɗai za ka sha wahala.”
-
13
Wawancin mace a bayyane yake; ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani.
-
14
Takan zauna a ƙofar gidanta, a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni,
-
15
tana kira ga masu wucewa, waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.
-
16
“Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!” Tana ce wa marasa hankali.
-
17
“Ruwan da aka sata ya fi daɗi; abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”
-
18
Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba.