📖 Karin Magana 8
-
1
Hikima ba ta yin kira ne? Fahimi ba ya tā da muryarsa ne?
-
2
A ƙwanƙoli a kan hanya, inda hanyoyi suka haɗu, ta ɗauki matsayinta;
-
3
kusa da ƙofofin shiga cikin birni, a mashigai, ta tā da murya,
-
4
“Gare ku, ya mutane, nake kira; na tā da muryata ga dukan ’yan adam.
-
5
Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali; ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi.
-
6
Ku saurara, gama ina da abubuwa masu darajan da zan faɗa; na buɗe leɓunana don in faɗa abin da yake daidai.
-
7
Bakina yana magana abin da yake gaskiya, gama leɓunana sun ƙi mugunta.
-
8
Dukan kalmomin bakina suna da adalci; babu waninsu da ya karkace ko kuwa ƙarya ne.
-
9
Ga mai tunani dukansu daidai ne; ba su da laifi ga waɗanda suke da sani.
-
10
Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa, sani a maimakon zinariya zalla,
-
11
gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja, kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita.
-
12
“Ni, hikima, ina zama tare da hankali; ina da sani da iya rarrabewa.
-
13
Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta; ina ƙin girman kai da fariya, halin mugunta da kuma muguwar magana.
-
14
Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne; ina da fahimi da kuma iko.
-
15
Ta wurina sarakuna suke mulki masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci;
-
16
ta wurina sarakuna suke mulki, da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.
-
17
Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, kuma waɗanda suke nemana sukan same ni.
-
18
Tare da ni akwai wadata da girmamawa, dukiya da wadata masu dawwama.
-
19
’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla; amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau.
-
20
Ina tafiya a hanyar adalci, a kan hanyoyin gaskiya,
-
21
ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata ina sa wuraren ajiyarsu su cika.
-
22
“ Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa, kafin ayyukansa na tuntuni;
-
23
an naɗa ni tun fil azal, daga farko, kafin duniya ta kasance.
-
24
Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni, sa’ad da babu maɓulɓulai masu ruwa;
-
25
kafin a kafa duwatsu a wurarensu, kafin tuddai ma, an haife ni,
-
26
kafin ya yi duniya ko gonaki ko wata ƙurar duniya.
-
27
Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa,
-
28
sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram,
-
29
sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa domin kada ruwaye su zarce umarninsa, da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya.
-
30
A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa. Na cika da murna kowace rana, kullum ina farin ciki a gabansa,
-
31
ina farin ciki da dukan duniyarsa ina murna da ’yan adam.
-
32
“Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.
-
33
Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima; kada ku ƙyale ta.
-
34
Mai albarka ne wanda ya saurare ni; yana tsaro kullum a ƙofofina, yana jira a ƙofar shigata.
-
35
Gama duk wanda ya same ni ya sami rai zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
-
36
Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa; dukan waɗanda suke ƙina suna ƙaunar mutuwa ke nan.”