📖 Karin Magana 7
-
1
Ɗana, ka kiyaye kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka.
-
2
Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu; ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka.
-
3
Ka daure su a yatsotsinka; ka rubuta su a allon zuciyarka.
-
4
Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,” ka kuma kira fahimi danginka;
-
5
za su kiyaye ka daga mazinaciya, daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali.
-
6
A tagar gidana na leƙa ta labule mai rammuka.
-
7
Sai na gani a cikin marasa azanci, na lura a cikin samari, wani matashi wanda ba shi da hankali.
-
8
Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta, yana tafiya a gefen wajen gidanta
-
9
da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa, yayinda duhun dare yana farawa.
-
10
Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi, saye da riga kamar karuwa shirye kuma don ta yaudare shi.
-
11
(Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya, ƙafafunta ba sa zama a gida;
-
12
wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali, tana yawo a kowace kusurwa.)
-
13
Sai ta kama shi ta rungume shi da duban soyayya a fuskarta ta ce,
-
14
“Ina da hadaya ta salama a gida; yau zan cika alkawarina.
-
15
Saboda haka na fito don in sadu da kai; na neme ka na kuma same ka!
-
16
Na lulluɓe gadona da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.
-
17
Na yayyafa turare a gadona da mur, aloyes da kuma kirfa.
-
18
Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe; bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna!
-
19
Mijina ba ya gida; ya yi tafiya mai nisa.
-
20
Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”
-
21
Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.
-
22
Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo
-
23
sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.
-
24
Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.
-
25
Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta.
-
26
Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.
-
27
Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.