📖 Karin Magana 6
-
1
Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi, in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani,
-
2
in maganarka ta taɓa kama ka, ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,
-
3
to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka; da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka, ka tafi ka ƙasƙantar da kanka; ka roƙi maƙwabcinka!
-
4
Ka hana kanka barci, ko gyangyaɗi a idanunka ma.
-
5
Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.
-
6
Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!
-
7
Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki,
-
8
duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
-
9
Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku?
-
10
Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,
-
11
talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi.
-
12
Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki,
-
13
wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa,
-
14
wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye
-
15
Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.
-
16
Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,
-
17
duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,
-
18
zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,
-
19
mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.
-
20
Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
-
21
Ka ɗaura su a zuciyarka har abada; ka ɗaura su kewaye da wuyanka.
-
22
Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa’ad da kake barci, za su lura da kai; sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.
-
23
Gama waɗannan umarnai fitila ne, wannan koyarwa haske ne, kuma gyare-gyaren horo hanyar rayuwa ce,
-
24
suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a daga sulɓin harshen mace marar aminci.
-
25
Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.
-
26
Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta, mazinaciya kuma takan farauci ranka.
-
27
Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa ba tare da rigunansa sun ƙone ba?
-
28
Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba?
-
29
Haka yake da wanda ya kwana da matar wani; babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci.
-
30
Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata don yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa.
-
31
Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai ko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa.
-
32
Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali; duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.
-
33
Dūka da kunya ne za su zama rabonsa, kuma kunyarsa za tă dawwama.
-
34
Gama kishi kan tā da hasalar miji, kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa.
-
35
Ba zai karɓi duk wata biya ba; zai ƙi cin hanci, kome yawansu.