📖 Karin Magana 5
-
1
Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata ka saurara da kyau ga kalmomin basirata,
-
2
don ka ci gaba da yin kome daidai leɓunanka za su adana sani.
-
3
Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma, maganarta tana da sulɓi fiye da mai;
-
4
amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya, mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.
-
5
Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa; sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari.
-
6
Ba ta wani tunanin rayuwa; hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.
-
7
Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; kada ku juye daga abin da nake faɗa.
-
8
Ku yi nesa da hanyarta, kana ku je kusa da ƙofar gidanta,
-
9
don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu da kuma shekarunku ga wani marar imani,
-
10
don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.
-
11
A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi, sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.
-
12
Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo! Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!
-
13
Ban yi biyayya da malamaina ba ko in saurari masu koyar da ni.
-
14
Na zo gab da hallaka gaba ɗaya a tsakiyar dukan taron.”
-
15
Ku sha ruwa daga tankinku, ruwa mai gudu daga rijiyarku.
-
16
In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje, rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?
-
17
Bari su zama naka kaɗai, don kada ka raba da baƙi.
-
18
Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka, bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.
-
19
Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani, bari mamanta su ishe ka kullum, bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.
-
20
Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali? Don me za ka rungume matar wani?
-
21
Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji, yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.
-
22
Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi; igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan.
-
23
Zai mutu saboda rashin ɗa’a yawan wawancinsa zai sa yă kauce.