📖 Karin Magana 4
-
1
Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi.
-
2
Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.
-
3
Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,
-
4
ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.
-
5
Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.
-
6
Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.
-
7
Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima. Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.
-
8
Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka; ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka.
-
9
Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.”
-
10
Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa, shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa.
-
11
Na bishe ka a hanyar hikima na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi.
-
12
Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe; sa’ad da kake gudu, ba za ka fāɗi ba.
-
13
Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce; ka tsare shi sosai, gama ranka ne.
-
14
Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye.
-
15
Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka.
-
16
Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta; ba su barci sai sun cuci wani.
-
17
Mugunta da ta’adi kamar ci da sha suke a gare su.
-
18
Hanyar adali kamar fitowar rana ce, sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka.
-
19
Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne; ba sa sanin abin da ya sa suke tuntuɓe.
-
20
Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa, ka saurara sosai ga kalmomina.
-
21
Kada ka bari su rabu da kai, ka kiyaye su a cikin zuciyarka;
-
22
gama rai ne ga waɗanda suke nemansu da kuma lafiya ga dukan jikin mutum.
-
23
Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka, gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.
-
24
Ka kau da muguwar magana daga bakinka; ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka.
-
25
Bari idanunka su dubi gaba sosai, ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.
-
26
Ka san inda ƙafafunka suke takawa ka bi hanyoyin da suke daram kawai.
-
27
Kada ka kauce dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.