📖 Karin Magana 31
-
1
¶ Maganganun Sarki Lemuwel, magana ce horarriya mahaifiyarsa ta koya masa,
-
2
“Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina! Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata!
-
3
Kada ka ba da ƙarfinka a kan mata, ƙarfinka ga waɗanda suka hallaka sarakuna.
-
4
“Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel, ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi, ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,
-
5
don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta, su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.
-
6
A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;
-
7
bari su sha su manta da talaucinsu kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.
-
8
“Yi magana domin bebaye, domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.
-
9
Yi magana a kuma yi shari’ar adalci; a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”
-
10
Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.
-
11
Mijinta yana da cikakken amincewa da ita kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.
-
12
Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakin ranta.
-
13
Takan zaɓi ulu da lilin ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.
-
14
Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa.
-
15
Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.
-
16
Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.
-
17
Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.
-
18
Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.
-
19
Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.
-
20
Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata.
-
21
Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri.
-
22
Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa; tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.
-
23
Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni inda yakan zauna a cikin dattawan gari.
-
24
Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.
-
25
Ƙarfi da mutunci su ne suturarta; za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.
-
26
Tana magana da hikima, kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.
-
27
Tana lura da sha’anin gidanta kuma ba ta cin abincin ƙyuya.
-
28
’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka; haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,
-
29
“Mata da yawa suna yin abubuwan yabo, amma ke kin fi su duka.”
-
30
Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe; amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
-
31
Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta, bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.