📖 Karin Magana 3
-
1
Ɗana, kada ka manta da koyarwata, amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,
-
2
gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa su kuma kawo maka wadata.
-
3
Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka.
-
4
Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane.
-
5
Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka;
-
6
cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
-
7
Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
-
8
Wannan zai ba wa jikinka lafiya yă kuma adana ƙasusuwanka.
-
9
Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
-
10
ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.
-
11
Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,
-
12
domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.
-
13
Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, mutumin da ya sami fahimi,
-
14
gama ta fi azurfa riba tana kuma da amfani fiye da zinariya.
-
15
Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.
-
16
Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.
-
17
Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi, dukan hanyoyinta kuma salama ne.
-
18
Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta; waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.
-
19
Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya, ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;
-
20
ta wurin sani aka rarraba zurfafa, gizagizai kuma suka zubo raɓa.
-
21
Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira, kada ka bar su su rabu da kai;
-
22
za su zama rai a gare ka, abin adon da zai gyara wuyanka.
-
23
Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya, ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;
-
24
sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba; sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.
-
25
Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya ko lalacin da yakan auka wa mugaye,
-
26
gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.
-
27
Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka.
-
28
Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu.
-
29
Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, wanda yake zama da aminci kusa da kai.
-
30
Kada ka zargi mutum ba dalili, sa’ad da bai yi laifi ba.
-
31
Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu.
-
32
Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi.
-
33
La’anar Ubangiji tana a gidan mugaye, amma yakan albarkaci gidan adali.
-
34
Yakan yi wa masu girman kai ba’a amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri.
-
35
Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.