📖 Karin Magana 29
-
1
Mutumin da ya ci gaba da taurinkai bayan an kwaɓe shi ba da daɗewa ba zai hallaka ba makawa.
-
2
Sa’ad da masu adalci suke cin nasara, mutane kan yi farin ciki sa’ad da mugaye suke mulki, mutane kan yi nishi.
-
3
Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa.
-
4
Ta wurin yin adalci sarki kan sa ƙasa tă yi ƙarƙo amma duk mai haɗama don cin hanci kan rushe ƙasar.
-
5
Duk wanda yake wa maƙwabcinsa daɗin baki yana sa wa ƙafafunsa tarko ne.
-
6
Mugun mutum tarko ne ta wurin zunubinsa, amma mai adalci zai iya rera ya kuma yi murna.
-
7
Masu adalci sun damu game da adalci don talakawa, amma mugaye ba su da wannan damuwa.
-
8
Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi.
-
9
In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa, wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba.
-
10
Masu kisankai sukan ƙi mutum mai mutunci su kuma nema su kashe mai aikata gaskiya.
-
11
Wawa yakan nuna fushinsa a fili, amma mai hikima kan kanne fushinsa.
-
12
In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye.
-
13
Matalauci da azzalumi suna da wannan abu ɗaya. Ubangiji ne yake ba dukansu gani.
-
14
In sarki yana hukunta talakawa da adalci kursiyinsa kullum zai kasance lafiya.
-
15
Sandar gyara kan ba da hikima, amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.
-
16
Sa’ad da mugaye suke cin nasara, haka zunubi zai yi ta ƙaruwa, amma masu adalci za su ga fāɗuwar waɗannan mutane.
-
17
Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama; zai ba ka farin cikin da kake so.
-
18
Inda ba wahayi, mutane kan kangare; amma masu albarka ne waɗanda suke kiyaye doka.
-
19
Ba a yi wa bawa gyara ta wurin magana kawai; ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba.
-
20
Ka ga mutum mai yin magana da garaje? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.
-
21
In mutum ya yi wa bawansa shagwaɓa tun yana yaro, zai jawo baƙin ciki a ƙarshe.
-
22
Mutum mai cika fushi yakan tā da faɗa, mai zafin rai kuma kan yi zunubai masu yawa.
-
23
Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa.
-
24
Duk wanda yake abokin ɓarawo abokin gāban kansa ne; yana jin sa yana ta rantsuwa, amma bai isa ya ce kome ba.
-
25
Jin tsoron mutum tarko ne, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.
-
26
Mutane sukan nemi samun farin jini daga wurin sarki, amma daga wurin Ubangiji ne mutum kan sami adalci.
-
27
Masu adalci suna ƙyamar masu rashin gaskiya; mugaye sukan yi ƙyamar masu aikata gaskiya.