📖 Karin Magana 26
-
1
Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi, haka girmamawa bai dace da wawa ba.
-
2
Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya, haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take.
-
3
Bulala don doki, linzami don jaki, sanda kuma don bayan wawaye!
-
4
Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa.
-
5
Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne.
-
6
Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa.
-
7
Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas haka karin magana yake a bakin wawa.
-
8
Kamar ɗaura dutse a majajjawa haka yake da girmama wawa.
-
9
Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu haka karin magana yake a bakin wawa.
-
10
Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.
-
11
Kamar yadda kare kan koma ga amansa, haka wawa kan maimaita wautarsa.
-
12
Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.
-
13
Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya, zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”
-
14
Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa, haka rago yake jujjuya a gadonsa.
-
15
Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.
-
16
Rago yana gani yana da hikima fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.
-
17
Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa.
-
18
Kamar yadda mahaukaci yake harbin cukwimai ko kibiyoyi masu dafi
-
19
haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!”
-
20
In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.
-
21
Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta, haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.
-
22
Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi; sukan gangara can cikin cikin mutum.
-
23
Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba haka leɓuna masu mugun zuciya.
-
24
Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa, amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci
-
25
Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi, gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.
-
26
Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya, duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.
-
27
In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki; in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.
-
28
Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai, daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.