📖 Karin Magana 25
-
1
¶ Waɗannan ƙarin karin maganar Solomon ne waɗanda mutanen Hezekiya sarkin Yahuda suka tara.
-
2
Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun; a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne.
-
3
Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi, haka zukatan sarakuna suka wuce a bincika.
-
4
Ka tace azurfa sai kayan su fito don maƙerin azurfa;
-
5
ka cire mugaye daga gaban sarki, kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci.
-
6
Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki, kada kuma ka nemi wa kanka wuri a cikin manyan mutane;
-
7
gara ya ce maka, “Ka hauro nan,” da a ƙasƙantar da kai a gaban wani mai makami. Abin da ka gani da idanunka
-
8
kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa, gama me za ka yi a ƙarshe in maƙwabcinka ya ba ka kunya?
-
9
In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama, kada ka tona asirin wani,
-
10
in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka ba za ka kuma taɓa rabuwa da wannan mummuna suna ba.
-
11
Kalmar da aka faɗa daidai tana kamar zubin zinariyar da aka yi a mazubin azurfa.
-
12
Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa.
-
13
Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika; ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi.
-
14
Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama haka mutumin da yake fariya a kan kyautan da ba ya bayarwa.
-
15
Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki, magana mai hankali kan karye ƙashi.
-
16
In ka sami zuma, ka sha isashe kawai, in ya yi yawa, za ka yi amai.
-
17
Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka yawan ganinka zai sa ya ƙi ka.
-
18
Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa.
-
19
Kamar haƙori mai ciwo ko yin tafiya da gurguwar ƙafa haka yake ga mai dogara da marasa aminci a lokacin wahala.
-
20
Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi, ko kuwa kamar zuba ruwan tsami a kanwa, haka yake da mai rera waƙoƙi ga mai baƙin ciki.
-
21
In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci; in yana jin ƙishi, ka ba shi ruwa ya sha.
-
22
Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa, Ubangiji kuma zai sāka maka.
-
23
Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi.
-
24
Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
-
25
Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji haka yake da jin labari mai daɗi daga ƙasa mai nisa.
-
26
Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace haka yake da mai adalci wanda ya miƙa wuya ga mugaye.
-
27
Ba shi da kyau ka sha zuma da yawa, haka ma ba shi da kyau ka nemi girma wa kanka.
-
28
Kamar birni da katangarsa sun rushe haka yake da mutumin da ba ya iya danne fushinsa.