1Kada ka yi ƙyashin mugaye, kada ka yi sha’awar ƙungiyarsu;
2gama leɓunansu suna maganar tā-da-na-zaune-tsaye ne.
3Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta;
4ta wurin sani ɗakunanta sukan cika da kyawawan kayayyaki masu daraja.
5Mutum mai hikima yana da iko sosai, kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi;
6don yin yaƙi kana bukatar bishewa, kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa.
7Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa.
8Duk mai ƙulla mugunta za a ɗauka shi mai kuta hargitsi ne.
9Makircin wawa zunubi ne, mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a.
10In ba ka da ƙarfi a lokacin wahala, ka tabbatar kai marar ƙarfi ne sosai!
11Ka kuɓutar da waɗanda ake ja zuwa inda za a kashe su; ka riƙe waɗanda suke tangaɗi zuwa wajen yanka.
12In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba?
13Ka sha zuma, ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau; zuma daga kaki yana da zaƙi a harshenka.
14Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai; in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
15Kada ka kwanta kana fako kamar ɗan iska don ƙwace gidan adali, kada ka ƙwace masa wurin zama;
16gama ko da adali ya fāɗi sau bakwai, yakan tashi kuma, amma bala’i kan kwantar da mugaye.
17Kada ka yi dariya sa’ad da abokin gāba ya fāɗi; sa’ad da ya yi tuntuɓe, kada ka yi farin ciki,
18in ba haka ba in Ubangiji ya gani ba zai amince ba ya kuma juye fushinsa daga gare shi.
19Kada ka ji tsoro saboda masu mugunta ko ka yi ƙyashin mugaye,
20gama mugu ba shi da zuciya ta nan gaba, kuma fitilar mugaye za tă mutu.
21Ka ji tsoron Ubangiji da kuma sarki, ɗana, kuma kada ka haɗa kai da masu tayarwa,
22gama za a tura waɗannan biyu zuwa hallaka nan da nan, kuma wa ya sani irin bala’in da za su iya kawowa?
23¶ Waɗannan ma maganganun masu hikima ne, Nunan sonkai a shari’a ba shi da kyau.
24Duk wanda ya ce wa mai laifi, “Ba ka da laifi”, mutane za su la’ance shi al’umma kuma za tă ce ba a san shi ba.
25Amma zai zama da lafiya ga duk waɗanda suka hukunta masu laifi, kuma babban albarka zai zo a kansu.
26Amsa da take ta gaskiya tana kamar sumba a leɓuna.
27Ka gama aikinka ka kuma shirya gonakinka; bayan haka, ka gina gidanka.
28Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba, ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu.
29Kada ka ce, “Zan yi masa kamar yadda ya yi mini; zan rama abin da wannan mutum ya yi mini.”
30Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;
31ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe.
32Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.
33Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,
34sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.