📖 Karin Magana 23
-
1
Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki, ka lura sosai da abin da yake gabanka,
-
2
ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka in kai mai ci da yawa ne.
-
3
Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi gama wannan abinci ruɗu ne.
-
4
Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa.
-
5
Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa.
-
6
Kada ka ci abincin mai rowa, kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi;
-
7
gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai.
-
8
Za ka yi amai ɗan abin da ka ci dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza.
-
9
Kada ka yi magana da wawa, gama zai yi wa maganar hikimarka ba’a.
-
10
Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā ko ka ɗiba gonar marayu,
-
11
gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi; zai kuwa yi magana dominsu.
-
12
Ka mai da hankali ga umarni ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani.
-
13
Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.
-
14
Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa.
-
15
Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce, to, zuciyata za tă yi murna;
-
16
cikin cikina zai yi farin ciki in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai.
-
17
Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi, amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi.
-
18
Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
-
19
Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima, ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.
-
20
Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci,
-
21
gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.
-
22
Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai, kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.
-
23
Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita; ka nemi hikima, horo da fahimi.
-
24
Mahaifin adali yana da farin ciki sosai; duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.
-
25
Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna; bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!
-
26
Ɗana, ka ba ni zuciyarka bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina,
-
27
gama karuwa rami ne mai zurfi mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce.
-
28
Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza.
-
29
Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?
-
30
Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.
-
31
Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!
-
32
A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.
-
33
Idanunka za su riƙa gane-gane, zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.
-
34
Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, kwance a sama itacen jirgin ruwa.
-
35
Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! Yaushe zan farka don in ƙara shan wani?”