📖 Karin Magana 22
-
1
An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa; tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.
-
2
Mawadaci da matalauci suna da abu guda. Ubangiji ne Mahaliccinsu duka.
-
3
Mai basira kan ga damuwa tana zuwa yă nemi mafaka, amma marar azanci kan yi ta tafiya yă kuma sha wahala.
-
4
Sauƙinkai da tsoron Ubangiji sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.
-
5
A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko, amma duk wanda ya kiyaye ransa kan kauce musu.
-
6
Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi, kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
-
7
Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.
-
8
Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala, za a kuma hallaka sandar fushinsa.
-
9
Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta.
-
10
Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje; fitina da zargi kuma za su ƙare.
-
11
Duk mai son tsabtar zuciya wanda kuma jawabinsa mai alheri ne zai zama aminin sarki.
-
12
Idanun Ubangiji na lura da sani, amma yakan ƙi kalmomin marar aminci.
-
13
Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!” Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”
-
14
Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi; duk wanda yake a ƙarƙashin fushin Ubangiji zai fāɗa a ciki.
-
15
Wauta tana da yawa a zuciyar yara, amma sandar horo zai kore ta nesa da su.
-
16
Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.
-
17
Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima; ka yi amfani da abin da nake koyarwa,
-
18
gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka ka kuma kasance da su a shirye a leɓunanka.
-
19
Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji, ina koya maka yau, har kai ma.
-
20
Ban rubuta maka maganganu talatin ba, maganganun shawara da sani,
-
21
ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai, saboda ka iya ba da amsa daidai ga duk wanda ya aike ka?
-
22
Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a,
-
23
gama Ubangiji zai yi magana dominsu zai kuwa washe waɗanda suka washe su.
-
24
Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,
-
25
in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko.
-
26
Kada ka zama mai ɗaukar lamuni ko ka ba da jingina saboda bashi;
-
27
gama in ka kāsa biya za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.
-
28
Kada ka matsar da shaidar kan iyakar da kakanninka suka kafa.
-
29
Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa? Zai yi wa sarakuna hidima; ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba.