📖 Karin Magana 21
-
1
A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne wanda yake bi da shi duk inda ya so.
-
2
Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke, amma Ubangiji yakan auna zuciya.
-
3
Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.
-
4
Girmankai da fariya, su ne fitilar mugaye, wannan kuwa zunubi ne!
-
5
Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci.
-
6
Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya tarin tururi ne da kuma mugun tarko.
-
7
Rikicin mugaye zai yi gāba da su, gama sun ƙi su yi abin da yake daidai.
-
8
Hanyar mai laifi karkatacciya ce, amma halin marar laifi sukan aikata gaskiya.
-
9
Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
-
10
Mugun mutum yakan zaƙu ya aikata mugunta; maƙwabcinsa ba ya samun jinƙai daga gare shi.
-
11
Sa’ad da aka hukunta mai ba’a marasa azanci suka yi wayo; sa’ad da aka yi wa mai hikima umarni yakan sami sani.
-
12
Mai Adalci kan lura da gidan mugu kan kuma zama sanadin lalacin mugu.
-
13
In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba.
-
14
Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi, kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani.
-
15
Sa’ad da aka yi adalci, yakan kawo farin ciki ga mai adalci amma fargaba ga masu aikata mugunta.
-
16
Mutumin da ya kauce daga hanyar fahimi kan zo ga hutu a ƙungiyar matattu.
-
17
Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci; duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba.
-
18
Mugu kan zama abin fansa don adali, marar aminci kuma don mai aikata gaskiya.
-
19
Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali.
-
20
A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau, amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.
-
21
Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna kan sami rai, wadata da girmamawa.
-
22
Mutum mai hikima kan fāɗa wa birnin jarumawa ya kuma rushe katangar da suka dogara a kai.
-
23
Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa.
-
24
Mai girmankai da kuma mai fariya, “Mai ba’a” ne sunansa; yana yin abubuwa da girmankai ainun.
-
25
Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.
-
26
Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake.
-
27
Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi!
-
28
Mai ba da shaidar ƙarya zai hallaka, kuma duk wanda ya saurare shi zai hallaka har abada.
-
29
Mugun mutum kan yi tsayin daka, amma mai aikata gaskiya kan yi tunani a kan abin da yake yi.
-
30
Babu hikima, babu tunani, babu shirin da zai yi nasara a kan Ubangiji.
-
31
Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne.