📖 Karin Magana 20
-
1
Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne; duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.
-
2
Fushin sarki yana kama da rurin zaki; duk wanda ya sa shi fushi zai rasa ransa.
-
3
Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.
-
4
Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.
-
5
Manufofin zuciyar mutum zurfafan ruwaye ne, amma mutum mai basira yakan jawo su.
-
6
Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne, amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda.
-
7
Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi; masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa.
-
8
Sa’ad da sarki ya zauna kan kujerarsa don yă yi shari’a, yakan ga dukan mugunta da idanunsa.
-
9
Wa zai iya cewa, “Na kiyaye zuciyata da tsarki; ni mai tsabta ne marar zunubi kuma”?
-
10
Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba, Ubangiji ya ƙi su duka.
-
11
Akan san ƙananan yara ta ayyukansu, ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta.
-
12
Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani, Ubangiji ne ya yi su duka.
-
13
Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.
-
14
“Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya; sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki.
-
15
Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace, amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja.
-
16
A karɓi rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
-
17
Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi, amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi.
-
18
Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara; in kana yaƙi, ka sami bishewa.
-
19
Mai gulma yakan lalace yarda; saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu.
-
20
In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, fitilarsa za tă mutu a tsakiyar duhu.
-
21
Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba.
-
22
Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!” Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka.
-
23
Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba, da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.
-
24
Ubangiji ne yake bi da matakan mutum, Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa?
-
25
Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.
-
26
Sarki mai hikima yakan gane mugunta; ya hukunta su ba tausayi.
-
27
Fitilar Ubangiji kan bincika zuciyar mutum takan bincika lamirinsa.
-
28
Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya; ta wurin ƙauna sarautarsa za tă zauna a kafe.
-
29
Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu, furfura ita ce darajar tsofaffi.
-
30
Naushi da rauni kan share mugunta, dūka kuma kan tsabtacce lamiri.