📖 Karin Magana 2
-
1
Ɗana, in ka yarda da kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
-
2
kana kasa kunne ga abin da yake na hikima, kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,
-
3
in kuma ka kira ga tsinkaya ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,
-
4
in ka neme shi yadda ake neman azurfa ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,
-
5
to, za ka gane tsoron Ubangiji ka kuma sami sanin Allah.
-
6
Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
-
7
Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya, shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
-
8
gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
-
9
Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.
-
10
Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka, sani kuma zai faranta maka rai.
-
11
Tsinkaya za tă tsare ka, ganewa kuma za tă yi maka jagora.
-
12
Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci,
-
13
waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,
-
14
waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci,
-
15
waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu.
-
16
Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,
-
17
wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.
-
18
Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu.
-
19
Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.
-
20
Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai.
-
21
Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar, marasa laifi kuma za su kasance a cikinta;
-
22
amma za a fid da mugaye daga ƙasar, za a tumɓuke marasa aminci kuma daga gare ta.