📖 Karin Magana 19
-
1
Gara matalauci wanda yake marar laifi da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.
-
2
Ba shi da kyau ka kasance da niyya babu sani, ko ka kasance mai garaje ka ɓace hanya.
-
3
Wautar mutum kan lalatar da ransa, duk da haka zuciyarsa kan ba wa Ubangiji laifi.
-
4
Wadata kan kawo abokai da yawa, amma abokin matalauci kan bar shi.
-
5
Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.
-
6
Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki, kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne.
-
7
’Yan’uwan matalauci sukan guje shi, balle abokansa, su ma za su guje shi. Ko da yake matalaucin yana binsu yana roƙo, ba zai sam su ba.
-
8
Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa; duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba.
-
9
Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka.
-
10
Bai dace da wawa ya yi rayuwa cikin jin daɗi ba, haka ya fi muni bawa ya yi mulki a kan sarki!
-
11
Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.
-
12
Fushin sarki yana kama da rurin zaki, amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa.
-
13
Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne, mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.
-
14
Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne, amma mace mai basira daga Ubangiji ne.
-
15
Ragwanci kan jawo zurfin barci, mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.
-
16
Duk wanda ya bi umarnai kan tsare ransa, amma duk wanda ya ƙi binsu zai mutu.
-
17
Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne, zai kuwa sami lada game da abin da ya yi.
-
18
Ka hori ɗanka, gama yin haka akwai sa zuciya; kada ka goyi baya lalacewarsa.
-
19
Dole mai zafin rai yă biya tara; in ka fisshe shi sau ɗaya, to, sai ka sāke yin haka.
-
20
Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni, a ƙarshe kuwa za ka yi hikima.
-
21
Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum, amma manufar Ubangiji ce takan cika.
-
22
Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa; gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci.
-
23
Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai. Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi.
-
24
Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa!
-
25
Ka bulale mai ba’a, marasa azanci kuwa za su yi la’akari; ka tsawata wa mai basira, zai kuwa ƙara sani.
-
26
Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci.
-
27
In ka daina jin umarni, ɗana, za ka kuwa kauce daga kalmomin sani.
-
28
Mai shaidar da yake malalaci yana wa shari’a ba’a ne, bakin mugaye kuma na haɗiye mugunta.
-
29
An shirya tara saboda masu ba’a ne, dūka kuma saboda bayan wawaye.