📖 Karin Magana 18
-
1
Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai; yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai.
-
2
Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.
-
3
Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo, haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo.
-
4
Kalmomin bakin mutum suna da zurfi kamar ruwaye, amma maɓulɓulan hikima rafi ne mai gudu.
-
5
Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri ko ka hana wa marar laifi adalci.
-
6
Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa, bakinsa kuma kan gayyaci dūka.
-
7
Bakin wawa lalatar da kansa yake yi leɓunansa kuma tarko ne ga ransa.
-
8
Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke; sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.
-
9
Wanda yake ragwanci a aikinsa ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.
-
10
Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi; masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
-
11
Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga; suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba.
-
12
Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai, amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
-
13
Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara, wannan wauta ce da kuma abin kunya.
-
14
Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo, amma in ya karai, to, tasa ta ƙare.
-
15
Zuciya mai la’akari kan nemi sani; kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya.
-
16
Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa yakan kuma kai shi a gaban babban mutum.
-
17
Wanda ya fara mai da jawabi yakan zama kamar shi ne mai gaskiya, sai wani ya fito ya yi masa tambaya tukuna.
-
18
Jefa ƙuri’a kan daidaita tsakanin masu faɗa ta kuma ajiye masu faɗan a rabe.
-
19
Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa, kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.
-
20
Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika; girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi.
-
21
Harshe yana da ikon rai da mutuwa, kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.
-
22
Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
-
23
Matalauci kan yi roƙo da taushi, amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya.
-
24
Mutum mai abokai masu yawa kan lalace, amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.