📖 Karin Magana 17
-
1
Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.
-
2
Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa.
-
3
Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.
-
4
Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna; maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.
-
5
Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne; duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi.
-
6
Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.
-
7
Leɓunan basira ba su dace da wawa ba, ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya!
-
8
Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi; ko’ina ya juye, yakan yi nasara.
-
9
Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.
-
10
Tsawata kan sa mutum ya koyi basira fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.
-
11
Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah; za a aika manzo mutuwa a kansu.
-
12
Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa.
-
13
In mutum ya sāka alheri da mugunta, mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba.
-
14
Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.
-
15
Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu.
-
16
Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa, da yake ba shi da sha’awar samun hikima?
-
17
Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.
-
18
Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci.
-
19
Duk mai son faɗa yana son zunubi, duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka.
-
20
Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba; duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala.
-
21
Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki babu farin ciki ga mahaifin wawa.
-
22
Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
-
23
Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce don yă lalace yin adalci.
-
24
Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima, amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya.
-
25
Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.
-
26
Ba shi da kyau a hukunta marar laifi, ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu.
-
27
Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi, mutum mai basira kuma natsattse ne.
-
28
Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.