📖 Karin Magana 16
-
1
Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke, amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.
-
2
Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi, amma Ubangiji yakan auna manufofi.
-
3
Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
-
4
Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa, har ma da mugaye domin ranar masifa.
-
5
Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.
-
6
Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi; ta wurin tsoron Ubangiji mutum kan guji mugunta.
-
7
Sa’ad da hanyoyin mutum sun gamshi Ubangiji, yakan sa abokan gāban mutumin ma su zauna lafiya da shi.
-
8
Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci da sami riba mai yawa ta hanyar rashin gaskiya.
-
9
’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu, amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.
-
10
Leɓunan sarki kan yi magana kamar ta wurin ikon Allah, kuma bai kamata bakinsa ya yi kuskure a yanke shari’a ba.
-
11
Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne; dukan ma’aunai da suke cikin jaka yinsa ne.
-
12
Sarakuna suna ƙyamar abin da ba shi da kyau, gama an kafa kujerar sarauta ta wurin adalci ne.
-
13
Sarakuna sukan ji daɗi leɓuna masu yin gaskiya; sukan darjanta mutumin da yake faɗin gaskiya.
-
14
Fushin sarki ɗan saƙon mutuwa ne, amma mai hikima yakan faranta masa rai.
-
15
Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan; tagomashinsa yana kamar girgijen ruwa a bazara.
-
16
Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya, ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!
-
17
Buɗaɗɗiyar hanyar masu aikata gaskiya kan guje wa mugunta; duk wanda yake lura da hanyarsa yakan lura da ransa.
-
18
Girmankai yakan zo kafin hallaka, girman kai yakan zo kafin fāɗuwa.
-
19
Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu sauƙinkai, da ka raba ganima da masu girman kai.
-
20
Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara, kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji.
-
21
Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai, kuma kalmomi masu daɗi kan inganta umarni.
-
22
Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi, amma wauta kan kawo hukunci ga wawaye.
-
23
Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa, kuma leɓunansa kan inganta umarni.
-
24
Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma, mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.
-
25
Akwai hanyar da ta yi kamar daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.
-
26
Marmarin cin abinci yakan yi wa ɗan ƙodago aiki; yunwarsa kan sa ya ci gaba.
-
27
Mutumin banza yakan ƙulla mugunta, kuma jawabinsa yana kama da wuta mai ƙuna.
-
28
Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.
-
29
Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa ya kai shi a hanyar da ba ta da kyau.
-
30
Duk wanda ya ƙyifce da idonsa yana ƙulla maƙarƙashiya ce; duk wanda ya murguɗa leɓunansa yana niyya aikata mugunta ke nan.
-
31
Furfura rawani ne mai daraja; akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.
-
32
Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi, ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.
-
33
Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.