📖 Karin Magana 15
-
1
Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.
-
2
Harshen mai hikima kan yi zance mai kyau a kan sani, amma bakin wawa kan fitar da wauta.
-
3
Idanun Ubangiji suna a ko’ina, suna lura da masu aikata mugunta da masu aikata alheri.
-
4
Harshen da ya kawo warkarwa shi ne itacen rai, amma harshe mai ƙarya kan ragargaza zuciya.
-
5
Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa, amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.
-
6
Gidan adali yana da dukiya mai yawa, amma albashin mugaye kan kawo musu wahala.
-
7
Leɓunan masu hikima sukan baza sani; ba haka zukatan wawaye suke ba.
-
8
Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye, amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi.
-
9
Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci.
-
10
Horo mai tsanani yana jiran duk wanda ya bar hanya; wanda ya ƙi gyara zai mutu.
-
11
Mutuwa da Hallaka suna nan a fili a gaban Ubangiji, balle fa zukatan mutane!
-
12
Mai yin ba’a yakan ƙi gyara; ba zai nemi shawara mai hikima ba.
-
13
Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske, amma ciwon zuciya kan ragargaza rai.
-
14
Zuciya mai la’akari kan nemi sani, amma bakin wawa wauta ce ke ciyar da shi.
-
15
Dukan kwanakin mutumin da ake danniya fama yake yi, amma zuciya mai farin ciki yana yin biki kullum.
-
16
Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.
-
17
Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take.
-
18
Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa.
-
19
An tare hanyar rago da ƙayayyuwa, amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce.
-
20
Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa, amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.
-
21
Wauta kan sa mutum marar azanci ya yi farin ciki, amma mai basira kan kiyaye abin da yake yi daidai.
-
22
Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara.
-
23
Mutum yakan yi farin ciki a ba da amsar da take daidai, kuma ina misali a yi magana a lokacin da ya dace!
-
24
Hanyar rai na yin jagora ya haura wa masu hikima don ta kiyaye shi daga gangarawa zuwa kabari.
-
25
Ubangiji yakan rushe gidan mai girman kai amma yakan kiyaye iyakokin gwauruwa daidai.
-
26
Ubangiji yana ƙyamar tunanin mugaye, amma waɗanda suke da tunani masu tsabta yakan ji daɗinsu.
-
27
Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa, amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu.
-
28
Zuciyar mai adalci takan auna amsoshinta, amma bakin mugu yakan fitar da mugunta.
-
29
Ubangiji yana nesa da mugaye amma yakan ji addu’ar adalai.
-
30
Fuska mai fara’a takan kawo farin ciki ga zuciya, kuma labari mai daɗi na kawo lafiya ga ƙasusuwa.
-
31
Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba.
-
32
Duk waɗanda suka ƙi horon sun rena kansu ke nan, amma duk waɗanda sun yarda da gyara sukan ƙara basira.
-
33
Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima, kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.