📖 Karin Magana 14
-
1
Mace mai hikima kan gina gidanta, amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.
-
2
Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji, amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi.
-
3
Maganar wawa kan kawo sanda a bayansa, amma leɓunan masu hikima kan tsare su.
-
4
Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome, amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito.
-
5
Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu, amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi.
-
6
Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome, amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira.
-
7
Ka guji wawa, gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.
-
8
Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu, amma wautar wawaye ruɗu ne.
-
9
Wawaye kan yi ba’a a gyaran zunubi, amma fatan alheri yana samuwa a cikin masu aikata gaskiya.
-
10
Kowace zuciya ta san ɓacin ranta, kuma babu wani dabam da zai yi rabon jin daɗinsa.
-
11
Za a rushe gidan mugu, amma tentin mai aikata gaskiya zai haɓaka.
-
12
Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.
-
13
Ko cikin dariya zuciya takan yi ciwo, kuma farin ciki kan iya ƙarasa a baƙin ciki.
-
14
Marasa bangaskiya za su sami sakamako cikakke saboda hanyoyinsu, kuma mutumin kirki zai sami lada saboda nasa.
-
15
Marar azanci kan gaskata kome, amma mai la’akari kan yi tunani game da matakinsa.
-
16
Mai hikima kan ji tsoron Ubangiji ya kuma guji mugunta, amma wawa yana da girman kai yakan yi kome da garaje.
-
17
Mutum mai saurin fushi yakan yi ayyukan wauta, akan kuma ƙi mai son nuna wayo.
-
18
Marar azanci kan gāji wauta, amma mai la’akari kan sami rawanin sani.
-
19
Masu mugunta za su rusuna a gaban masu kirki, mugaye kuma za su yi haka a ƙofofin adalai.
-
20
Maƙwabta sukan gudu daga matalauta, amma masu arziki suna da abokai da yawa.
-
21
Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata.
-
22
Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci.
-
23
Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.
-
24
Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu, amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai.
-
25
Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka, amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne.
-
26
Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka, kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.
-
27
Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.
-
28
Yawan mutane shi ne ɗaukakar sarki, amma in ba tare da mabiya ba sarki ba kome ba ne.
-
29
Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa, amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.
-
30
Zuciya mai salama kan ba jiki rai, amma kishi kan sa ƙasusuwa su yi ciwo.
-
31
Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.
-
32
Sa’ad bala’i ya auku, mugaye kan fāɗi, amma ko a mutuwa masu adalci suna da mafaka.
-
33
Hikima tana a zuciyar mai azanci, kuma ko a cikin wawaye takan sa a santa.
-
34
Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane.
-
35
Sarki yakan yi murna a kan bawa mai hikima, amma bawa marar kunya kan jawo fushinsa.