📖 Karin Magana 13
-
1
Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa, amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.
-
2
Daga abin da ya fito leɓunan mutum ne mutum kan ji daɗin abubuwa masu kyau, amma marar aminci yakan ƙosa ya tā-da-na-zaune-tsaye.
-
3
Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa, amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci.
-
4
Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.
-
5
Adali yana ƙin abin da yake ƙarya, amma mugu kan jawo kunya da ƙasƙanci.
-
6
Adalci yakan lura da mutum mai mutunci, amma mugunta takan sha kan mai zunubi.
-
7
Wani mutum yakan ɗauki kansa mai arziki ne, alhali ba shi da kome, wani ya ɗauki kansa shi matalauci ne, alhali shi mawadaci ne ƙwarai.
-
8
Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa, amma matalauci ba ya jin barazana.
-
9
Hasken masu adalci kan haskaka ƙwarai, amma fitilar mugaye mutuwa take.
-
10
Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.
-
11
Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
-
12
Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo, amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
-
13
Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa, amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada.
-
14
Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne, mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.
-
15
Fahimta mai kyau kan sami tagomashi, amma hanyar marar aminci tana da wuya.
-
16
Kowane mai azanci yakan nuna sani, amma wawa yakan yi tallen wawancinsa.
-
17
Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala, amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa.
-
18
Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya, amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.
-
19
Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai, amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta.
-
20
Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima, amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
-
21
Rashin sa’a kan fafare mai zunubi, amma wadata ce ladar adali.
-
22
Mutumin kirki kan bar gādo wa ’ya’ya ’ya’yansa, amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci.
-
23
Gonar matalauci za tă iya ba da abinci a yalwace, amma rashin adalci kan share shi tas.
-
24
Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba, amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.
-
25
Masu adalci sukan ci isashen abinci, amma cikin mugaye na fama da yunwa.