📖 Karin Magana 12
-
1
Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani, amma duk mai ƙin gyara wawa ne.
-
2
Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji, amma Ubangiji yakan hukunta mai son yin wayo.
-
3
Ba yadda mutum zai kahu ta wurin aikata mugunta, amma ba za a tumɓuke adali ba.
-
4
Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne, amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa.
-
5
Shirye-shiryen masu adalci daidai ne, amma shawarar mugaye ruɗu ne.
-
6
Kalmomin mugu sukan kwanta suna jira su yi kisankai, amma jawabin masu aikata gaskiya kan kuɓutar da su.
-
7
Akan tumɓuke mugaye ba a ƙara ganinsu, amma gidan masu adalci kan tsaya daram.
-
8
Akan yabi mutum bisa ga hikimarsa, amma mutane marasa azanci akan rena su.
-
9
Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa da ka mai da kanka kai wani ne alhali kuwa ba ka da abinci.
-
10
Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa, amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta.
-
11
Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.
-
12
Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane, amma saiwar masu adalci kan haɓaka.
-
13
Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi, amma adali kan kuɓuta daga wahala.
-
14
Daga abubuwan da suke fitowa daga leɓunansa mutum kan cika da abubuwa masu kyau tabbatacce yadda aikin hannuwansa suke ba shi lada.
-
15
Hanyar wawa daidai take a gare shi, amma mai hikima kan saurari shawara.
-
16
Wawa kan nuna fushinsa nan take, amma mai la’akari kan ƙyale zargi.
-
17
Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya, amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.
-
18
Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.
-
19
Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada, amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.
-
20
Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.
-
21
Ba wani lahanin da zai sami masu adalci, amma mugaye suna da nasu cike da wahala.
-
22
Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
-
23
Mai la’akari kan kiyaye saninsa wa kansa, amma zuciyar wawa kan yi ta tallar wawanci.
-
24
Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.
-
25
Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum, amma maganar alheri kan faranta masa rai.
-
26
Adali yakan yi hankali a abokantaka, amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.
-
27
Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta, amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci.
-
28
A hanyar adalci akwai rai; a wannan hanya akwai rashin mutuwa.