📖 Karin Magana 10
-
1
¶ Karin maganar Solomon. Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
-
2
Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.
-
3
Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu.
-
4
Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.
-
5
Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.
-
6
Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani, amma rikici kan sha bakin mugu.
-
7
Tunawa da mai adalci albarka ne amma sunan mugu zai ruɓe.
-
8
Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni amma surutun wawa kan kai ga lalaci.
-
9
Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.
-
10
Shi da ya ƙyifta ido da mugunta kan jawo baƙin ciki surutun wawa kuma kan zo da lalaci.
-
11
Bakin adali maɓulɓulan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.
-
12
Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.
-
13
Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi, amma bulala domin bayan marasa azanci ne.
-
14
Mai hikima kan yi ajiyar sani, amma bakin wawa kan gayyaci lalaci.
-
15
Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu, amma talauci shi ne lalacin matalauci.
-
16
Hakkin adalai kan kawo musu rai, amma albashin mugaye kan kawo musu hukunci.
-
17
Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai, amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.
-
18
Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa, duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.
-
19
Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki, amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.
-
20
Harshen adali azurfa ce zalla, amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani.
-
21
Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci.
-
22
Albarkar Ubangiji kan kawo wadata, ba ya kuma ƙara wahala a kai.
-
23
Wawa yakan ji daɗi halin mugunta, amma mutum mai fahimi kan ji daɗin hikima.
-
24
Abin da mugu ke tsoro shi ne zai same shi; abin da adali ke bukata yakan sami biyan bukata.
-
25
Sa’ad da hadiri ya taso, yakan watsar da mugaye, amma adalai za su tsaya daram har abada.
-
26
Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu, haka malalaci yake ga wanda ya aike shi.
-
27
Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai, amma akan gajartar da shekarun mugaye.
-
28
Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki, amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome.
-
29
Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta.
-
30
Ba za a taɓa tumɓuke masu adalci ba, amma mugaye ba za su ci gaba da kasance a ƙasar ba.
-
31
Bakin adalai kan fitar da hikima, amma za a dakatar da mugun harshe.
-
32
Leɓunan adalai sun san abin da ya dace, amma bakunan mugaye sun san abin da yake mugu ne kawai.