1¶ Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.
2Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo; don ganewa kalmomi masu zurfi;
3don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali, kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;
4don sa marar azanci yă yi hankali, yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,
5bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu, bari masu tunani kuma su sami jagora,
6don su fahimci karin magana da kuma misalai, kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.
7Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da horo.
8Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
9Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
10Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.
11In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;
12mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
13za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;
14ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”
15ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;
16gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai.
17Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye!
18Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko; ba sa kama kome, sai rayukansu!
19Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau; ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu.
20Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi, tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;
21tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu, tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.
22“Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi?
23Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina.
24Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,
25da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,
26Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,
27sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.
28“Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.
29Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,
30da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,
31za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.