1Da ma za ka tsage sammai ka sauko, ai, da duwatsu za su yi rawar jiki a gabanka!
2Kamar sa’ad da wuta takan ci rassa ta sa ruwa ya tafasa, ka sauko ka sanar da sunanka ga abokan gābanka ka kuma sa al’ummai su yi rawan jiki a gabanka!
3Gama sa’ad da ka aikata abubuwan bantsoron da ba mu sa tsammani ba, ka sauko, duwatsu kuma suka yi rawar jiki a gabanka.
4Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji, babu kunnen da ya gane, babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai, wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi.
5Kakan taimaki waɗanda suke murnan yin abin da yake daidai, waɗanda sukan tuna da hanyoyinka. Amma sa’ad da muka ci gaba da yin zunubi, kakan yi fushi. Ta yaya za mu sami ceto ke nan?
6Dukanmu mun zama kamar wanda yake marar tsabta, kuma dukan ayyukanmu masu adalci sun zama kamar ƙazaman tsummoki; duk mun zama kamar busasshen ganye, kamar iska haka zunubanmu sukan share mu.
7Babu wanda yake kira bisa sunanka ko ya yi ƙoƙarin riƙe ka; gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu ka kuma sa muka lalace saboda zunubanmu.
8Duk da haka, Ubangiji, kai ne Ubanmu. Mu yumɓu ne, kai kuma mai ginin tukwane; dukanmu aikin hannunka ne.
9Kada ka yi fushi fiye da kima, ya Ubangiji; kada ka tuna da zunubanmu har abada. Da ma ka dube mu, muna roƙonka, gama dukanmu mutanenka ne.
10Biranenka masu tsarki sun zama hamada; har Sihiyona ma ta zama hamada; Urushalima ta zama kango.
11Haikalinmu mai tsarki da kuma mai daraja, inda kakanninmu suka yabe ka, an ƙone da wuta, kuma dukan abubuwan da muke ƙauna sun lalace.
12Bayan dukan wannan, ya Ubangiji, ba za ka yi wani abu ba? Za ka yi shiru ka hore mu fiye da kima?