1Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai; zai sāke zaɓi Isra’ila yă kuma zaunar da su a ƙasarsu. Baƙi ma za su zo su zauna tare da su su haɗa kai da gidan Yaƙub.
2Al’ummai za su ɗauke su su kuma kawo wurin da yake nasu. Gidan Isra’ila kuwa za tă mallaki al’ummai a matsayin bayi maza da mata a ƙasar Ubangiji. Za su mai da waɗanda suka kama su su zama kamammu su kuma yi mulki a kan waɗanda suka taɓa danne su.
3¶ A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta,
4za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a. Mai danniya ya zo ga ƙarshe! Dubi yadda fushinsa ya ƙare!
5Ubangiji ya karye sandar mugaye, sandan mulkin masu mulki,
6wanda cikin fushi ya kashe mutane da bugu marar ƙarewa, kuma cikin fushi ya mamaye al’ummai da fushi ba ƙaƙƙautawa.
7Dukan ƙasashe suna hutawa suna kuma cikin salama; sun ɓarke da waƙa.
8Har itatuwan fir ma da kuma al’ul na Lebanon suna murna a kanka suna cewa, “Yanzu da aka ƙasƙantar da kai, babu wani mai yankan katakon da ya zo yă yanka mu.”
9Kabari a ƙarƙashi duk ya shirya don yă sadu da kai a zuwanka; yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka, dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya; ya sa suka tashi daga kujerun sarauta, dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai.
10Duk za su amsa, za su ce maka, “Ashe kai ma raunana ne, kamar mu; ka zama kamar mu.”
11An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari, tare da surutan garayunka; tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka tsutsotsi kuma suka rufe ka.
12Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!
13Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.
14Zan haura can bisa gizagizai; zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.”
15Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami.
16Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido, suna tunani abin da zai same ka. “Wannan mutumin ne ya girgiza duniya ya kuma sa mulkoki suka razana,
17mutumin da ya mai da duniya ta zama hamada, wanda ya tumɓuke biranenta bai kuma bar kamammunsa suka tafi ba?”
18Dukan sarakunan duniya suna kwance a mace, kowa a kabarinsa.
19Amma an jefar da kabarinka kamar reshen da aka ƙi; an rufe ka da waɗanda aka kashe, tare da waɗanda aka soke da takobi, waɗanda suka gangara zuwa duwatsun rami. Kamar gawar da aka tattake da ƙafa,
20ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba, gama ka hallaka ƙasarka ka kuma kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaci zuriyarka masu aikata mugunta ba.
21A shirya wuri don a yayyanka ’ya’yansa maza saboda zunuban kakanninsu; kada a reno su su gāji ƙasar su cika duniya da biranensu.
22“Zan yi gāba da su,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta, ’ya’yanta da zuriyarta,” in ji Ubangiji.
23“Zan mai da ita wuri domin mujiyoyi da kuma fadama; zan share ta da tsintsiyar hallaka,” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
24¶ Ubangiji Maɗaukaki ya rantse, “Tabbatacce, kamar yadda na riga na shirya, haka zai kasance, kuma kamar yadda na nufa, haka zai zama.
25Zan ragargazar da Assuriya a cikin ƙasata; a kan duwatsuna zan tattake shi. Za a ɗauke nauyin da ya sa wa mutanena, a kuma ɗauke nauyinsa daga kafaɗunsu.”
26Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya; wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan.
27Gama Ubangiji Maɗaukaki ya ƙudura ya yi wannan, wa kuwa zai hana shi? Ya riga ya miƙa hannunsa, wa zai komar da shi?
28¶ Wannan abin da Allah ya yi magana ya zo ne a shekarar da Sarki Ahaz ya mutu.
29Kada ku yi farin ciki, dukanku Filistiyawa, cewa sandar da ta buge ku ta karye; daga saiwar wannan maciji wani mugun maciji mai dafi zai taso, ’ya’yansa za su zama wani maciji masu dafi mai tashi sama.
30Mafi talauci na matalauta zai sami wurin kiwo, mabukata kuma za su kwana lafiya. Amma zan hallakar da saiwarka da matsananciyar yunwa; za tă kashe naka da suka rage da rai.
31Ki yi ihu, ya ke ƙofa! Yi kururuwa, ya ke birni! Ku razana, dukanku Filistiyawa! Ƙunshin hayaƙi yana tasowa daga arewa, kuma babu matsorata a cikin sojojinsa.
32Wace amsa ce za a bayar wa jakadun wannan al’umma? “ Ubangiji ya kafa Sihiyona, kuma a cikinta mutanensa masu shan azaba za su sami mafaka.”