1¶ Sa’ad da Musa ya gama kafa tabanakul, sai ya shafe shi da mai, ya tsarkake shi tare da dukan kayayyakinsa, ya kuma shafe bagaden da mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.
2Sa’an nan shugabannin Isra’ila, wato, shugabannin iyalai waɗanda suke shugabancin kabilan da aka ƙidaya, suka miƙa hadayu.
3Suka kawo kyautansu a gaban Ubangiji. Kyautayin kuwa su ne, kekunan yaƙi shida da aka rufe, da shanu goma sha biyu, saniya guda daga kowane shugaba, da kuma keken yaƙi guda daga shugabanni biyu. Suka miƙa waɗannan a gaban tabanakul.
4¶ Ubangiji ya ce wa Musa,
5“Ka karɓi abubuwan nan daga gare su, domin a yi amfani da su a aikin Tentin Sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”
6¶ Haka fa Musa ya ɗauki kekunan yaƙi da shanun ya ba wa Lawiyawa.
7Ya ba wa Gershonawa, kekunan yaƙi biyu da shanu huɗu bisa ga aikinsu,
8ya kuma ya ba wa kabilar Merari kekunan yaƙi huɗu da shanu takwas bisa ga aikinsu. Aka ba da su duka a ƙarƙashin ikon Itamar ɗan Haruna, firist.
9Amma Musa bai ba wa Kohatawa kome ba, gama aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.
10¶ Sa’ad da aka shafe bagaden da mai, sai shugabannin suka kawo hadayunsu saboda keɓewarsa, suka miƙa su a bagaden.
11Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa, “Kowace rana, shugaba guda zai kawo hadayarsa saboda keɓewar bagade.”
12Wanda ya kawo hadayarsa a rana ta farko shi ne Nashon ɗan Amminadab, shugaban mutanen Yahuda.
13Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri ne, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
14ya kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
15da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
16ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
17da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Nashon ɗan Amminadab.
18A rana ta biyu, Netanel ɗan Zuwar, shugaban mutanen Issakar, ya kawo hadayarsa.
19Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
20ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel, goma cike da turaren hayaƙi;
21da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
22ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
23da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Netanel ɗan Zuwar.
24A rana ta uku, Eliyab ɗan Helon, shugaban mutanen Zebulun, ya kawo hadayarsa.
25Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
26ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
27da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
28ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
29da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyab ɗan Helon.
30A ranan ta huɗu, Elizur ɗan Shedeyur, shugaban mutanen Ruben, ya kawo hadayarsa.
31Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
32ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
33da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
34ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
35da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elizur ɗan Shedeyur.
36A rana ta biyar, Shelumiyel ɗan Zurishaddai, shugaban mutanen Simeyon, ya kawo hadayarsa.
37Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
38ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
39da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
40ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
41da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Shelumiyel ɗan Zurishaddai.
42A rana ta shida, Eliyasaf ɗan Deyuwel, shugaban mutanen Gad, ya kawo hadayarsa.
43Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
44ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
45da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
46ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
47da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyasaf ɗan Deyuwel.
48A rana ta bakwai, Elishama ɗan Ammihud, shugaban mutanen Efraim, ya kawo hadayarsa.
49Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
50kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
51da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
52ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
53da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elishama ɗan Ammihud.
54A rana ta takwas, Gamaliyel ɗan Fedazur, shugaban mutanen Manasse, ya kawo hadayarsa.
55Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
56kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
57da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
58ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
59da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Gamaliyel ɗan Fedazur.
60A rana ta tara, Abidan ɗan Gideyoni, shugaban mutanen Benyamin, ya kawo hadayarsa.
61Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
62kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
63da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
64ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
65da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Abidan ɗan Gideyoni.
66A rana ta goma, Ahiyezer ɗan Ammishaddai, shugaban mutanen Dan, ya kawo hadayarsa.
67Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
68kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
69da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
70ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
71da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahiyezer ɗan Ammishaddai.
72A rana ta goma sha ɗaya, Fagiyel ɗan Okran, shugaban mutanen Asher, ya kawo hadayarsa.
73Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
74kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
75da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
76ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
77da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Fagiyel ɗan Okran.
78A rana ta goma sha biyu, Ahira ɗan Enan, shugaban mutanen Naftali, ya kawo hadayarsa.
79Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
80kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
81da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
82ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
83da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahira ɗan Enan.
84Waɗannan su ne hadayun shugabannin Isra’ilawa saboda keɓewar bagade sa’ad da aka shafe shi, an kawo faranta goma sha biyu na azurfa, darunan goma sha biyu na azurfa don yayyafawa, da kuma kwanonin zinariya goma sha biyu.
85Kowane faranti na azurfa yana da nauyin shekel ɗari da talatin, kuma kowane daro na azurfa don yayyafawa yana da nauyin shekel saba’in. Duka-duka dai, nauyin kwanonin azurfa, shekel dubu biyu ne da ɗari huɗu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
86Kwanonin zinariya goma sha biyu da aka cika da turaren hayaƙi kuwa, nauyinsu shekel goma ne kowanne, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Duka-duka dai, nauyin kwanonin zinariya, shekel ɗari ɗaya ne da ashirin.
87Jimillar dabbobi don hadaya ta ƙonawa, ta kai ƙanana bijimai goma sha biyu, raguna goma sha biyu da ’yan raguna goma sha biyu, dukansu bana ɗaya-ɗaya, tare da hadayarsu ta hatsi. Aka yi amfani da bunsurai goma sha biyu domin hadaya don zunubi.
88Jimillar dabbobi don hadaya ta salama, ta kai shanu ashirin huɗu, raguna sittin, bunsurai sittin da kuma ’yan raguna sittin, dukansu bana ɗaya-ɗaya. Waɗannan su ne hadayu saboda keɓewar bagade, bayan an shafe shi.
89¶ Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yă yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana.