2Ya Ubangiji, na ji irin shaharar da ka yi; na yi al’ajabi game da ayyukanka, ya Ubangiji. Ka maimaita su a kwanakinmu, ka sanar da su a lokacinmu; ka yi jinƙai ko a lokacin da kake fushi.
3Allah ya zo daga Teman, Mai Tsarkin nan daga Dutsen Faran. Sela Ɗaukakarsa ta rufe sammai yabonsa kuma ya cika duniya.
4Darajarsa ta yi kamar fitowar rana; ƙyalƙyali ya wulga daga hannunsa, inda ikonsa yake a ɓoye.
5Annoba ta sha gabansa; cuta kuma tana bin bayansa.
6Ya tsaya, ya kuwa girgiza duniya; ya duba, sai ya sa al’ummai suka yi rawan jiki. Tsofaffin duwatsu sun wargaje daɗaɗɗun tuddai kuma suka rurrushe. Hanyoyinsa dawwammamu ne.
7Na ga tentin Kushan cikin azaba; wuraren zaman Midiyan cikin damuwa.
8Ka ji haushin koguna ne, ya Ubangiji? Ko kuwa ka hasala da rafuffuka ne? Ko ka yi fushi da teku ne sa’ad da ka hau dawakanka da kuma kekunan yaƙinka masu nasara?
9Ka ja bakanka, ka nemi a ba ka kibiyoyi masu yawa. Sela Ka raba duniya da koguna;
10duwatsu sun gan ka sai suka ƙame. Ruwaye masu hauka sun yi ta fantsamawa; zurfafa suka yi ruri suka tā da raƙuman ruwansu sama.
11Rana da wata suka tsaya cik a sammai da ganin kibiyoyinka masu wucewa fyu, da ganin hasken māshinka mai walƙiya.
12Cikin hasala ka ratsa duniya cikin fushi kuma ka tattake ƙasashe.
13Ka fito don ka fanshi mutanenka, don ceci shafaffenka. Ka ragargaza shugaban ƙasar mugaye, ka tuɓe shi daga kai har ƙafa. Sela
14Da māshinsa ka soki kansa sa’ad da jarumawansa suka fito don su tarwatse mu, suna farin ciki sai ka ce masu shirin cinye matalautan da suke a ɓoye.
15Ka tattake teku da dawakanka, kana kaɗa manyan ruwaye.
16Na ji sai zuciyata ta buga, leɓunana sun yi rawa da jin murya; ƙasusuwana suka ruɓe, ƙafafuna kuma sun yi rawa. Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.
17Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba, ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi, ko da yake zaitun bai ba da amfani ba, gonaki kuma ba su ba da abinci ba, ko da yake babu tumaki a garke, ba kuma shanu a turaku,
18duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, zan yi murna da Allah Mai Cetona.
19Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina; yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa, yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi.