📖 Farawa 5
-
1
¶ Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah.
-
2
¶ Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.”
-
3
Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set.
-
4
Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
-
5
Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu.
-
6
Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh.
-
7
Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
-
8
Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu.
-
9
Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan.
-
10
Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
-
11
Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu.
-
12
Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel.
-
13
Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata
-
14
Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu.
-
15
Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared.
-
16
Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata
-
17
Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu.
-
18
Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok.
-
19
Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
-
20
Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu.
-
21
Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela.
-
22
Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
-
23
Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365.
-
24
Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
-
25
Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek.
-
26
Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
-
27
Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu.
-
28
Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa.
-
29
Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.”
-
30
Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da ’ya’ya maza da mata.
-
31
Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu.
-
32
Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.