2“Ɗan mutum, da me itacen kuringa ya fi reshen waɗansu itatuwa kyau a cikin kurmi?
3An taɓa ɗaukan itacensa an yi wani abu mai amfani? Akan yi maratayi da ita da za a rataya wani abu a kai?
4Bayan kuma a jefa ta cikin wuta, wuta kuma ta cinye kowane gefe ta kuma babbaka tsakiyarta, tana da amfani don yin wani abu kuma?
5In ba ta da amfanin wani abu sa’ad da take cikakkiya, balle bayan da wuta ta babbake ta, za a iya yin amfani da ita?
6¶ “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kamar yadda na ba da itacen kuringa a cikin itatuwan kurmi ya zama itacen wuta, haka zan sa mazaunan Urushalima su zama.
7Zan yi gāba da su. Ko da yake sun fito daga wuta, wuta za tă cinye su. Kuma sa’ad da na yi gāba da su, za ku san cewa ni ne Ubangiji.
8Zan mai da ƙasar kufai domin sun yi rashin aminci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”