📖 Ayuba 9
-
1
¶ Sai Ayuba ya amsa,
-
2
“Lalle, na san wannan gaskiya ne. Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?
-
3
Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi, ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu.
-
4
Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?
-
5
Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani kuma yana juya su cikin fushinsa.
-
6
Yana girgiza ƙasa, yana girgiza harsashenta.
-
7
Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske; yana hana taurari yin haske.
-
8
Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku.
-
9
Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza, da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.
-
10
Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.
-
11
Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni; ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce.
-
12
Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’
-
13
Allah ba ya danne fushinsa; ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su.
-
14
“Ta yaya zan iya yin faɗa da shi? Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi?
-
15
Ko da yake ba ni da laifi, ba zan iya amsa masa ba; sai dai roƙon jinƙai zan iya yi ga mahukuncina.
-
16
Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba.
-
17
Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili.
-
18
Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba.
-
19
In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?
-
20
Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.
-
21
“Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina.
-
22
Ba bambanci; shi ya sa na ce, ‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’
-
23
Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.
-
24
Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan?
-
25
“Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri; suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu.
-
26
Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.
-
27
‘In na ce zan manta da abin da yake damu na, zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’
-
28
duk da haka ina tsoron duk wahalata, domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba.
-
29
Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi, duk ƙoƙarina a banza yake.
-
30
Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda,
-
31
duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.
-
32
“Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa, har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a.
-
33
In da akwai wanda zai iya shiga tsakaninmu, ya ɗora hannunsa a kanmu tare,
-
34
wani wanda zai sa Allah yă daina duka na, don yă daina ba ni tsoro.
-
35
Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba, amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba.