📖 Ayuba 8
-
1
¶ Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,
-
2
“Har yaushe za ka gama faɗa waɗannan abubuwa? Maganganunka ba su da amfani.
-
3
Allah ba mai shari’ar gaskiya ba ne? Ko Maɗaukaki yakan yi abin da ba daidai ba?
-
4
Lokacin da ’ya’yansa suka yi masa zunubi, yakan bar su su sha wahalar da zunubi yake kawowa.
-
5
Amma in za ka dubi Allah ka roƙi Maɗaukaki,
-
6
in kai mai tsarki ne, kuma mai adalci, ko yanzu ma zai taimake ka, yă mayar maka iyalinka da farin cikinka.
-
7
Ko da yake za ka fara da kaɗan, duk da haka za ka gama da samu mai yawa.
-
8
“Tambayi na gaba da kai ka ji abin da iyayenka suka koya
-
9
gama jiya kaɗai aka haife mu ba mu san kome ba, kuma kwanakinmu a duniya masu wucewa ne.
-
10
Ba za su bishe ka su kuma gaya maka abin da za ka yi ba? Ba za su yi magana daga cikin hikimar da suke da ita ba?
-
11
Ko kyauro zai iya yi girma a wurin da ba ruwa? Ko za tă taɓa iya yin girma ba tare da ruwa ba?
-
12
Yayinda take girma ba a yanka ta, takan mutu da sauri fiye da ciyawa.
-
13
Abin da yake faruwa ke nan da duk wanda yake mantawa da Allah; waɗanda ba su da Allah, ba su da bege.
-
14
Abin da yake dogara a kai ba shi da ƙarfi; abin da yake dogara a kai yanar gizo ce.
-
15
Ya jingina ga yanar gizo, amma ba ta tare shi, sun kama ta, amma ba za tă taimake su tsayawa ba.
-
16
Yana kama da shukar da aka ba ta ruwa sosai lokacin da akwai rana sosai, tana yaɗuwa da kyau;
-
17
shukar tana bin yaɗuwa, jijiyoyinta suna nannaɗe duwatsu, suna neman wurin da za su kama sosai a cikin duwatsu.
-
18
Amma lokacin da aka tuge shukar daga wurin da take, wurin ba zai san da ita kuma ba, wurin zai ce, ‘Ban taɓa ganin ki ba.’
-
19
Ba shakka shukar ta mutu ke nan, kuma waɗansu za su tsiro a wurin.
-
20
“Ba shakka, Allah ba ya ƙin marar laifi, ko kuma yă ƙarfafa masu aikata mugunta.
-
21
Sai dai yă cika bakinka da dariya, yă sa ka yi sowa ta murna.
-
22
Maƙiyanka za su sha kunya, za a kawar da tentin mugaye.”