📖 Ayuba 7
-
1
“Mutum bai sha wahalar aiki ba a duniya? Rayuwarsa ba kamar ta wanda aka yi hayarsa ba ne?
-
2
Kamar yadda bawa yakan jira yamma ta yi, ko kuma kamar yadda wanda aka yi hayarsa yakan jira a biya shi kuɗin aikin da ya yi.
-
3
Saboda haka rabona shi ne watanni na zama banza, kowane dare kuwa sai ɓacin rai nake samu.
-
4
Lokacin da na kwanta ina tunani, ‘Har sai yaushe zan tashi?’ Gari ya ƙi wayewa, ina ta jujjuyawa har safe.
-
5
Jikina duk tsutsotsi da ƙuraje sun rufe shi, fatar jikina ta ruɓe tana fitar da ruwan miki.
-
6
“Kwanakina suna wucewa da sauri, fiye da yadda ƙoshiyar masaƙa take wucewa da sauri, za su kawo ga ƙarshe ba bege.
-
7
Ka tuna, ya Allah, raina numfashi ne kawai; idanuna ba za su taɓa sāke ganin farin ciki ba.
-
8
Idanun da suke ganina yanzu ba za su sāke ganina ba; za ku neme ni amma ba za ku same ni ba.
-
9
Kamar yadda girgije yakan ɓace yă tafi, haka mutum yake shige zuwa kabari ba kuwa zai dawo ba.
-
10
Ba zai taɓa zuwa gidansa ba; ba za a sāke san da shi ba.
-
11
“Saboda haka ba zan yi shiru ba; zan yi magana cikin ɓacin raina, zan nuna ɓacin raina cikin ruhu, cikin ƙuncin raina.
-
12
Ni teku ne, ko kuwa dodon ruwa, don me kake tsaro na?
-
13
Lokacin da nake zato zan sami salama in na kwanta a gadona don in huta,
-
14
duk da haka kana ba ni tsoro da mafarke-mafarke, kana tsorata ni da wahayi.
-
15
Na gwammace a shaƙe ni in mutu maimakon in kasance cikin wannan jiki.
-
16
Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada. Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani.
-
17
“Mene ne mutum har da ka kula da shi haka, har ka mai da hankali a kansa,
-
18
har kake duba shi kowace safiya, kake kuma gwada shi koyaushe?
-
19
Ba za ka ɗan daina kallo na ba ko ka rabu da ni na ɗan lokaci?
-
20
In na yi zunubi, me na yi maka, kai mai lura da mutane? Don me ka sa ni a gaba? Na zame maka kaya mai nauyi ne?
-
21
Me ya sa ba za ka gafarta mini laifofina ba? Gama na kusa kwantawa cikin ƙasa; za ka neme ni, amma ba za ka same ni ba.”