📖 Ayuba 5
-
1
“Ka yi kira in kana so, amma wa zai amsa maka? Wurin waɗanne tsarkaka za ka juya?
-
2
Fushi yana kashe wawa, ƙyashi kuma yana kashe marar azanci.
-
3
Ni ma na ga wawa yana cin gaba, amma nan da nan gidansa ya zama la’ananne.
-
4
’Ya’yansa suna cikin hatsari, ba wanda zai tsaya musu a gaban alƙali,
-
5
mayunwata sun kwashe girbinsa, har abubuwan da suke cikin ƙaya, masu jin ƙishirwa kuma suna zuba ido ga dukiyarsa.
-
6
Gama ba daga cikin ƙasa wahala take fitowa ba, ko kuma bala’i daga ƙasa.
-
7
Duk da haka an haifi mutum don wahala ne, kamar yadda ba shakka tartsatsin wuta yake tashi.
-
8
“Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata.
-
9
Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa.
-
10
Yana zuba ruwan sama a ƙasa; yana zuba ruwa a gonaki.
-
11
Yana ɗaukaka masu sauƙinkai, yana kāre waɗanda suke makoki.
-
12
Yana dagula shirye-shiryen masu wayo don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi.
-
13
Yana kama masu wayo cikin wayonsu, yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba.
-
14
Da rana sukan yi karo da duhu; da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke.
-
15
Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi; yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.
-
16
Saboda haka matalauta suna da bege, rashin gaskiya kuma ta yi shiru.
-
17
“Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.
-
18
Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.
-
19
Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka.
-
20
Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi.
-
21
Zai kāre ka daga ɓata suna, kuma ba ka bukata ka ji tsoro in hallaka ta zo.
-
22
Za ka yi wa hallaka da yunwa dariya; kuma ba ka bukata ka ji tsoron manyan namun jeji.
-
23
Gama za ka zauna lafiya da duwatsu a gonaki, kuma manyan namun jeji za su yi zaman salama da kai.
-
24
Za ka zauna lafiya a cikin tenti naka, za ka ƙirga kayanka za ka samu kome na nan.
-
25
Za ka san cewa ’ya’yanka za su zama da yawa, zuriyarka kuma kamar ciyawa a ƙasa.
-
26
Za ka yi kyakkyawan tsufa kafin ka mutu, kamar yadda ake tara dammuna a lokacin girbi.
-
27
“Mun yi nazarin wannan, kuma gaskiya ne. Saboda haka ka ji, ka kuma yi amfani da shi.”